Fulani makiyaya sun kashe wani bafulace dan fashi sun kai bindigarsa gidan gwamnati

Wasu Fulani makiyaya a jihar Zamfara,sun aika wani Bafulatani barzahu bayan ya tare hanya da bindiga kirar Ak47 yana yi wa jama'a fashi a kusa da kauyen Kango da ke Dansadau a karamar hukumar Maru a jihar Zamfara ranar Lahadi.

Mujallar isyaku.com ya samo cewa Fulani makiyaya suna kiwon dabbobinsu ne sai suka sami labari cewa wani Bafulace ya tare hanya da bindiga yana yi was jama'a fash.

Nan take suka hada Kansu suka nufi wajen da yake, bayan sun bukaci ya mika wuya sai ya ki, daga bisani harbe harbe ya kaure tsakaninsu da daya bafulatani kuma suka kashe shi, suka dauko bindigarsa kirar AK47 suka kai gidan Gwamnatin Zamfara.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post