Duba abinda wani Gwamnan arewa ya yi bayan yan bautan kasa 2 sun mutu a hadarin mota

Wani hadarin mota da ya faru a kauyen Gobirawa da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina ya yi sanadin mutuwar wasu matasa masu bautan kasa guda biyu.


Mujallar isyaku.com ya samo cewa hadarin ya auku ne yayin da direban motar ya taka burki kasancewa ana ruwan sama kuma titi ya jike da ruwa, sai motar ta kwace wa direban ta je ta daki wani itace da ke cikin daji.
Yan bautan kasar da suka mutu sun hada da wata budurwa daga jihar Akwa Ibom da kuma wani saurayi daga jihar Anambra, sai dai NYSC na jihar Katsina bata bayar da sunayen mamatan ba kawo lokacin buga wannan rahotu.
Hakazalika Gwamna Aminu Masari wanda ke kan hanyarsa ta zuwa garin Danja, ya umurci motar PILOT na tawagarsa ta kwashi gawaki da sauran yan bautan kasa da suka sami rauni aka kaisu Katsina .

Yan bautan kasar suna kan hanyarsu ne na zuwa daurin aure a Funtua cikin motar bas na yan bautan kasa mai lamba MAN 45 AA.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post