Da zafinsa! An kama gawurtaccen mai garkuwa da mutane nan Wadume a TarabaLegit Hausa

Rahotanni daga jaridar Premium Times sun tabbatar mana da cewa an sake kama rikakken mai garkuwa da bil’adama a jihar Taraba wato Hamisu Wadume. Babu cikakkaen bayani game da hakikanin wurin da aka kai Wadume, amma sai dai majiyar da ta samar da wannan labarin ta ce an kama shi ne a ranar Talata.

Majiyar da ta fitar da wannan labarin ta gano Wadume ne hedikwatar ‘yan sandan Najeriya dake Abuja ranar Talata. Ana sa ran samun cikakken bayani kama Wadume daga wurin hukumar ‘yan sanda nan bada jimawa ba. Idan baku manta ba a ranar 6 ga watan Agusta ne wata tawagar kwararrun jami’an ‘yan sanda su ka kama Wandume wanda ya samu kubuta bayan anyi musayar wuta tsakanin ‘yan sanda da sojoji.

A sakamakon musayar wutan har mutum hudu sun mutu wadanda uku daga cikinsu jami’an ‘yan sanda ne. Jami’an ‘yan sandan na tafe da shi ne a hanyarsu ta zuwa Jalingo kafin aukuwar wannan lamari. Aukuwar wannan al’amarin ya janyo ka-ce na-ce tsakanin sojoji da ‘yan sanda da kuma al’ummar Najeriya. Wannan dalilin ne ya sanya Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin gaggawa game da yin bincike a kan gaskiyar lamarin.

Kwamitin binciken wanda aka baiwa makonni biyu domin kammala bincike ya nemi kari wasu makonnin biyu inda ya kamata a ce bincike nasu ya kare cikin makon da ya gabata. Kamitin binciken na kunshe ne da jami’an sojoji da na ‘yan sanda. Kawowa yanzu an kama jami’ai sama da 25 wadanda ake zarginsu da hannu wurin taimakawa Hamisu Wadume.


DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post