Da dumi dumi: Kotu ta aika sammaci ga AGF da EFCC kan dukiyar Yari

Legit Hausa
Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja a ranar Litinin, 26 ga watan Agusta ta aika sammaci ga Atoji Janar na tarayya da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) akan su gurfana a gabanta a ranar Alhamis, akan lamarin da ya shafi kayayyaki da dukiyoyin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulazeez Yari.
An bukaci su zo sannan su nuna dalilin da yasa ba za su janye daga daskarar da asusun bankinsa ko kwace kayayyakinsa ba a Najeiya har zuwa lokacin da za a saurar kararsa da yanke hukunci ba.
Justis Nkeonye Maha ya bayar da umurnin bayan sauraron korafe-korafen da ke cikin karar daga lauyan Yari, Mahmud Magaji (SAN).
An gabatar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/948/2019, domin nuni ga sashi na 46(1) da (3) na kundin tsarin mulkin 1999 da odar da ke tattare da hukunci na 3 da 4 na dokar yanci na 2009.
Justis Maha ya kuma yi umurni ga a aika takardar sammaci ga mutanen a cikin sa’o’i 48 sannan ya dage zaman zuwa ranar Alhamis na wannan mako.
DAGA ISYAKU.COM Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post