Bashir Magashi: Bayan satan makudan kudi a baya, ya zama babban ministan Buhari - Rahoto

Legit Hausa
Jaridar Premium Times ta saki wani rahoto mai ban tsoro kan daya daga cikin manyan ministocin da shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar a ranar Laraba, 21 ga Agusta, 2019.
Rahoton ya bayyana cewa a matsayinsa na babban jami'in Soja, ya ci amanar kasa inda aka kamashi dumu-dumu da babakere. Yayinda ya gano cewa anyi ram da shi, da bayyanannun hujjoji, sai ya nemi yadda aka sulhu ya biya cin hanci.
A lokacin, ya roki masu mulki su yafe masa amma zai basu kashi biyu cikin ukun dukiyar da ya handama kuma ya boye a wani asusun bakin kasar wajen.
Saboda kada mutuncinsa ya zube kuma kada hukuma ta garkameshi, sai suka amince suka karbi kudaden kuma suka bari ya ji dadin sauran cikin kwanciyar hankali.
Amma Bashir Magashi, Manjo Janar mai murabus - bayan wannan abu da yayi da satan kudi akalla $550,000 lokacin da yake mulki, ya dawo gwamnati kuma ya samu matsayin mai tsoka.
A ranar Laraba, shugaba Muhammadu Buhari ya daura masa nauyin shugabantan ma'aikatar tsaro, ma'aikata mafi kudi na uku cikin dukkan ma'aikatun gwamnati.
Bashir Salihi Magashi, mai shekaru 74 da haihuwa, ya kasance tsohon gwamnan jihar Sokoto (1990-1992) kuma aka nadashi kwamanda a Satumban 1993, gabanin kwace mulkin da Abacha yayi a Nuwamba.
Shin shugaba Muhammadu Buhari na sane da wannan zargi da ake yiwa Bashir Magashi kafin nadashi Minista? Wani jami'in fadar shugaban kasa ya bayyana cewa "Ina tabbatar muku da cewa babu yadda shugaban kasa zai san irin wannan abu kuma ya nada shi."
DAGA ISYAKU.COM Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post