An yi ma wani soji koran kare daga aiki bayan ya kashe dan acaba

Rundunar sojin Najeria ta 82 ta yi ma wani karamin soji mai suna Lance Cpl. Ajayi Johnson koran kare daga aikin soja bayan ta same shi da laifin kashe wani dan acaba mai suna Mr. Chimaobi Nwogu saboda ya ki ya bayar da N100 na goro a wajen da sojan ke aiki ranar 7 ga watan Agusta 2019, a Umoukereke Ngwa da ke karamar hukumar Obingwa a jihar Abia.

Mataimakin daraktan hulda da jama'a na rundunar Col. Aliyu Yusuf ne ya shaida wa manema labarai haka a birnin Enugu ranar Laraba.

Ya kara da cewa rundunar soji ta gurfanar  da Lance Cpl. Ajayi a gaban Kotunta na cikin gida, bayan an same shi da laifi, an rage masa mukami zuwa kurtun soji, daga bisani aka yi masa koran Kare daga aikin soji, kuma aka mika shi ga rundunar yansandan jihar Abia domin fuskantar tuhuma.
 .
DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post