An tasa keyan yansanda 4 zuwa Kurkuku sakamakon kashe samari 2

Wata Kotun Majistare da ke Ebute Metta a birnin Ikko, watau Lagos, ta tasa keyan wasu jami'an yansanda hudu zuwa Kurkuku bayan sun kashe wasu samari biyu da ake zargi da satan wayan salula a wajen tsayawar mota ta Ipaye a Lagos ranar 19 ga watan Agusta.

Jami'an yansandan sun hada da Omomuyiwa Fabiyi, 42; Solomon Olaniyi, 41; Sunday Solomon, 41; and Mukaila Aliyu, 35 duk an tasa keyarsu zuwa Kurkukun .Ikoyi har zuwa ranar 23 ga watan Satumba kafin lokacin da za a sami shawara daga ofishin DPP na jihar Lagos.

Wannan ya biyo bayan wani faifen bidiyo ne da ya zagaya  shafukan sada zumunta inda aka ga yansandan sun kama wasu samari kuma suka harbe su nan take bisa zargin satan wayan salula. Sakamakon haka ne hukumar yansandan jihar Lagos ta dauki matakin hukunta yansandan sakamakon aikata kisan gilla.

DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

shiga seniorapost.com domin samun labaran Turanci 
Previous Post Next Post