Fatima diyar Dangote ta haifi diya mace a kasar waje


Legit Hausa

Mun samu labari cewa ‘Diyar babban Mai kudin Najeriya Aliko Dangote watau Fatima Dangote, ta samu karuwa inda ta haifi jaririya. Jaridar The Cable ta rahoto wannan labari 12 ga Agusta, 2019. Da alamu an yi wannan haihuwa ne a cikin ‘yan kwanakin nan inda labarin ya fara ratsa gari a farkon makon nan. Hakan na zuwa ne kusan bayan shekara guda da rabi da a ka yi aurensu.

Fatima Dangote ta bar Najeriya ne zuwa Amurka a karshen makon da ya wuce. Dangote ta haihu ne a kasar wajen. Sahibin Mijin na ta wani babban Matukin jirgin sama ne wanda ya shahara. Hajiya Dangote ta na auren Jamilu Abubakar ne wanda Mahaifinsa ya taba riken mukamin babban Sufetan ‘yan sanda a Najeriya. Jamilu shi ne babban Yaron Muhammad D. Abubakar Fatima da Halima su na cikin ‘Ya ‘yan Dangote.

Attajirin ya na matukar Kaunar wadannan ‘Ya ‘ya na sa kamar yadda ya bayyana a ranar auren Fatima da Jamilu wanda ya ce ya dauka tamkar 'Da. A lokacin da a ka yi auren na su, Mai kudin Duniya, Bill Gates ya samu zuwa, haka kuma shugaban kasar Ghana Nana Akufo Addo da Attajirin nan na Nahiyar Afrika, Mo Ibrahim sun zo.

Manyan ‘yan siyasan gida da su ka halarci bikin da a ka yi a bara sun hada shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bukola Saraki, Yakubu Dogara. Sarakuna irin su Rilwan Akiolu, sun halarta. Read more: https://hausa.legit.ng/1253954-an-samu-karuwa-fatima-dangote-ta-haihu-a-kasar-amurka.html
 

DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN