An sace wani dan majalisar dokoki na jihar Sokoto

Wani rahotu daga jihar Sokoto ya ce an sace wani dan majalisar dokoki na jihar Sokoto Aminu Magaji Bodai, wanda shi ne ke wakiltan Dange/ Shuni a majalisar dokoki na jihar.

Wani danuwansa ya ce an sace Aminu ne da misalin karfe 1:15 na safe tsakain garin Dange da Bodai ranar Alhamis.

Kakakin yansandan jihar Sokoto Muhammed Sadiq Abubakar ya tabbatar da faruwar lamari, sai dai ya ce har yanzu ba'a gama tantance bayanai ba kan lamarin.
 
DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Previous Post Next Post