An kashe wata mata mai juna biyu aka cire jariri da ke cikinta (Hotuna)

Wadansu jama'a  a birnin Enugu sun gudanar da zanga zanga bayan an gano gawar wata mata mai dauke da juna biyu an kasheta kuma aka cire jariri da yake cikinta a Nchatancha Nike da ke Enugu ta gabas.

Ana zargin cewa wasu makiyaya ne suka kashe matan, sakamakon haka matasan yankin suka datse babban hanyar Enugu zuwa Abakaliki domin nina fushinsu.

Ita dai matar an ce tana dawowa ne daga gona lokacin da wannan tsautsayi ya rutsa da ita a hannun makiyayan.


DAGA ISYAKU.COM

Latsa Shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp

https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Shiga seniorapost.com domin saamun labaran turanci 
Previous Post Next Post