Legit Hausa
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa mambobin kungiyar Shi’a sun harbi wasu jami’an yan sanda da ke bakin aiki a majalisar dokokin kasar.
Lamarin ya haddasa tashin hankali a cikin harabar majalisar.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa anyi gaggawan daukar daya daga cikin jami’an yan sandan zuwa asibitin majalisar dokokin da miusalin karfe 1:55 na rana.
Idon shaida da dama da ke wajen, sun bayyana cewa lamarin ya afku ne a lokacin da masu zanga-zangar suka yi kokarin kutsa kai cikin majalisar ta karfin tuwo.
“Sun harbi jami’an yan sanda uku. Daya daga cikinsu ma kamar ya mutu,” inji wani idon shaida.
A daidai lokacin kawo wannan rahoton, jami’an yan sanda sun rufe mashigin majalisar dokokin yayinda karan harbi a sama ya karade ko ina.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi