Yanzu yanzu: Shugaba Buhari ya yi wani sabon nadi mai muhimmanci


Legit Hausa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mista Ahmed Bolaji Nagode a matsayin Darakta Janar na cibiyar horar da harkar wutar lantarki na kasa (NAPTIN). A wata wasika da ke tabbatar da nadin daga ma’aikatar wutar lantarki mai kwanan wata 18 ga watan Yuli, 2019 dauke da lamba FMP/7858/I/126, nadin zai shafe tsawon shekaru hudu ne.

Sannan kuma ya fara aiki ne daga ranar 20 ga watan Yuni, 2019. An haifi Bolaji Nagode a ranar 10 ga watan Augusta, 1962, sannan ya yi karatu a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, jami’ar Ilorin da kuma jami’ar Lagas.

Bolaji ya kasance mataimakin Janar Manaja a kamfanin wutar lantarki na Najeriya kafin daga bisani aka nada shi mataimakin darakta a cibiyar NAPTINS a watan Fabrairun 2013. Ya kuma zama darakta a watan Fabrrairun 2014-2016. Ya kasance rike da mukamin mukaddashin darakta janar na NAPTIN tun daga 2016 kafin wannan sabon nadin da aka yi masa.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post