Yanzu Yanzu: Shaidan Atiku ya yarda cewar sun biya sojoji N10,000 a lokacin zabe


Legit Hausa

Wani shaida da aka kira a gaban kotun sauraron korafe-korafen zaben Shugaban kasa ya yarda cewar shi da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun biya N10,000 ga wasu sojoji a lokacin zaben kasar da ya gabata.

Suleiman Mohammed Bulama, wanda yace yayi aiki a matsayin jami’in tattara sakamako a rumfar zabe na PDP a karamar hukumar Jika, ya bayar da bayani game da biyan N10,000 a rubutacciyar jawabinsa, inda ya karbi bakin a ranar Litinin, 15 ga watan Yuli a gaban kotun zaben

A lokacin amsa tambayoyi daga lauyan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alex Izinyon (SAN), Bulama wanda ya kasance shaidar wadanda ke kara, yace yana nanakan ikirarinsa na cewa shi da jam’iyyarsa sun biya n10,000 gaa wasu sojoji a zaben Shugaban kasa da ya gabata. Da izinyon ya tunkaree si cewa abunda suka yi cin hanci suka ba jami’an tsaron, shaidan yace a’a.

TALLA:   Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi

“Ba mu biya cin hanci ba.” A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Rundunar yan sandan Zamfara ta karyata labarin kaofin watsa labarai na kai wa shaidun dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar hari a jihar.

Lauyan Atiku ya fada ma kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban kasa a zaman karshe da suka yi cewa an far ma shaidun da hari a hanyarsu na zuwa Abuja daga Zamfara. Sai dai kuma, jami’in hulda da jama’a na runndunar, SP Muhammad Shehu, ya bayyana a jawabin da ya saki a ranar Lahadi, 14 ga watan Yuli a Gusau cewa babu rikodin hari makamancin haka a jihar. Kakakin rundunar ya bayyana ikirarin a matsayin mai batarwa.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN