Yanzu-yanzu: Sanatoci sun tantance Tanko Muahmmad a matsayin Alkalin Alkalai


Legit Hausa

Mukaddashin shugaban Alkalan Najeriya, Jastis Tanko Muhammad, ya dira majalisar dokokin tarayyar domin amsa tambayoyi da tabbatar da shi matsayin Alkalan alkalan Najeriya na din-din-din. Ya isa majalisar misalan karfe goma da minti goma kuma a yanzu nan misalin karfe 11:09, majalisar ta shirya shigowarsa cikin zauren majalisa.

Majalisar ta shiga ganawar sirri domin tattaunawa da Jastis Tanko Mohammed da kuma tabbatar da shi. Wannan ya sabawa ka'ida da al'adar majalisar saboda a zauren majalisa ake tantance duk wanda shugaban kasa ya gabatar matsayin shugaban alkalan Najeriya.

A yanzu haka, Sanatocin sun dawo daga ganawar sirri kuma mukaddashin Alkalin alkalan ya fara masa tambayoyi daga yan majalisan. A ranar Alhamis, shugaba Muhammadu Buhari ya aika wasika majalisar dattawa inda ya bukaci sanatocin sun tabbatar da Tanko Muhammad matsayin shugaban Alkalan Najeriya na din-din-din.

Wannan ya biyo bayan takardar majalisar koli ta shari'a wacce ta bukaci Buhari ya zamar da Tanko Mohammad cikakken Alkalin alkalai. Shugaba Buhari ya nada Alkali Tanko Mohammed a watan Junairu bayan dakatad da tsohon Alkalin alkalai, Walter Onnoghen, wanda aka tuhuma da zargin boye kadarorinsa
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN