Yanzu Yanzu: Kotun zabe tayi watsi da karar da ke kalubalatar nasarar Gwamna Bagudu


Legit Hausa

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamna da ke zama a Birnin Kebbi, babbar birnin jihar Kebbi, a ranar Litinin, 22 ga watan Yuli, tayi watsi da karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta shigar inda yake kalubalantar nasarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takararta, Gwamna Atiku Bagudu a zaben gwamna na 2019 da aka yi.

Da yake yanke hukunci, shugabar kotun zaben, Justis Amina Adamu Aliyu da ke jagorantar sauran alkalai biyu ta tabbatar da cewa karar da PDP ya shigar bai da muhimman hujjojin da ake bukata, wanda sai iya bayyana zaben a matsayin wanda ke cike da magudi kamar yadda PDP da dan takararta, Sanata Isa Galaudu suka yi ikirari.

Don haka justis Amina Aliyu, ta bayyana cewa an soke shari’an kan rashin inganci. Da yake martani akan hukuncin, lauyan Gwamna Bagudu da APC, Yakubu Maikiyau SAN, ya fada wa manema labarai a wata hira cewa hukuncin da alkalan kotun zaben suka yanke yana bisa ka’ida, inda ya Kara da cewa dashi da tawagarsa na lauyoyi sun ji dadi. Maikyau, ya kuma bayyana cewa idan har PDP bata gamsu da hukuncin ba tana iya garzayawa kotun daukaka kara, cewa hakan ba zai janye hankalinsu ba sai dai ma su bisu.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post