Legit Hausa
Kotun daukaka karar zaben gwamna dake zamanta a jihar Kano,
ta dakatar da bukatar dan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP, Abba Kabiru
Yusuf, ta gudanar da sauye-sauye a jerin sunayen shaidun da zasu tsaya masa a
gabanta. Dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar PDP, ya shigar da
bukatarsa a gaban kotun na neman samun dama ta sauya kurarai a cikin jerin
sunayen shaidun da za su tsaya masa a gabanta.
Abba K Yusuf na neman kotu da ta bashi damar kara sunayen
wasu shaidu takwas kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito. Babban lauya mai
wakilcin dan takarar na jam'iyyar PDP, Adegboyega Awomolo, ya ce babu wani nufi
na sauya sunayen shaidun da suka gabatar face bukatar kara sunayen wasu shaidun
takwas da a halin yanzu kotun ta ki amincewa.
Yayin shimfida dalilai da take zartar da hukunci, Mai
shari'a Halima S. Muhammad, ta ce kotun ta yi watsi da wannan bukata ta
jam'iyyar PDP duba da girma da kuma bijirowarta a kurarren lokaci da ya sabawa
ka'ida ta shari'a. Har ila yau, dan takarar gwamnan jihar Kano na jam'iyyar
PDP, Abba Kabir Yusuf, na ci gaba da kalubalantar nasarar da gwamna Abdullahi
Umar Ganduje yayi a babban zaben kasa da ya gudana a watan Maris da ya gabata
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi