Yanzu Yanzu: Hayaniya ya kaure a majalisar wakilai kan zabar Shugaban marasa rinjaye


Legit Hausa

A yanzu haka majalisar wakilai ya kaure da hayaniya kan sanar da matsayin Shugaban marasa rinjaye a majalisar. Rigiman ya fara ne kan hukuncin da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya yanke shawarar yin jifa da wata wasika daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ke zabar Kingsley Chinda a matsayin Shugaban marasa rinjaye.

Kakakin majalisar yayi gaban kansa wajen sanar da Ndudi Elumelu a matsayin Shugaban marasa rinjaye, lamarin da ya haddasa zanga-zanga daga mambobin PDP. Wani dan majalisa da ba a bayyana ba ya kwace sandar iko wanda hakan ya haddasa hayaniya. Jam’iyyar adawa a wata wasika ta bayyana Mista Chinda a matsayin shugabanta a majalisar wakilai.

Hukuncin jam’iyyar na kunshe ne a wata wasika mai kwanan wata 26 ga Yuni sannan ta mika ta zuwa ga kakakin majalisar. An tura wasika makamanciyar wannan zuwa majalisar dattawa, kan wanda jam’iyyar ke so ya zama shugabanta inda ta zabi Eyinnaya Abaribe a matsayin Shugaban masu rinjaye.

Jam’iyyar ta kasance mara rinjaye a majalisar wakilan, sannan kuma daga Mista Chinda har Elumelu mambobinta ne. Jam’iyyar PDP ta bukaci mambobinta da kada su zabi Mista Gbajabiamila a lokacin da yake takarar kujerar kakakin majalisar. Sai dai ba a san ko dalilin kakakin majalisar na aikata hakan na da nasaba da kokarin rama abunda PDP tayi masa ba.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN