Yan bindiga sun yi awon gaba da wani babban Sakataren gwamnati a wata jihar Arewa

Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da Sakataren dindindim na ma'aikatar ma'adanai da albarkatun kasa na jihar Adamawa Mr. Emmanuel Piridimso da safiyar Laraba 10 ga watan Yuni a gidansa da ke Jimeta da misalin karfe 3:30 na dare.

Wata majiya daga iyalinsa ta ce yan bindigan sun kai samame ne a gidan Emmanuel da ke rukunin gidaje na Clerk suka tafi da shi.

Kakakin rundunar yansandan jihar Adamawa Suleiman Yahaya ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya kuma ce yanzu haka har an tura jami'an yansanda na musamman domin kamo batagarin tare da ceto wanda aka kama.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN