Yan bindiga sun kashe jami'an yansanda 2 da ke rakiyar kudi zuwa Banki. Hotuna

Rundunar yansandan jihar Rivers ta ce ta kama mutum tara bisa zargin kisan wasu jami'an yansanda Mopol guda biyu da aka yi ranar 1 ga watan Juli a yankin Mile 2 da ke birnin Port Harcourt.

Yansandan suna aiki ne a wani Kampanin barasa da ake kira "Paddy Man" da ke unguwar Nwachukwu/Ojoto a birnin na Port Harcourt da ke jihar Rivers, kuma suna kan hanyarsu ne na zuwa Banki dauke da kudi tare da wasu ma'aikatan kampanin, kwatsam sai yan bindiga suka tsare su suka buda masu wuta.

Kakakin hukumar yansanda na jihar River Nnamdi Omoni ya ce bayan faruwar lamarin, jami'an yansanda na jihar Rivers sun kaddamar da farautar wadanda suka aikata laifin kuma har sun cafke su.


DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN