Yan bindiga sun kashe DPO da yansanda 3 har da mace yarsanda mai juna biyu

Da sanyin safiyar Litinin wasu yan bindiga sun kai mumunar hari a caji ofis na yansanda da ke Agudama- Ekpetiama a jihar Bayelsa suka kashe jami'an yansanda hudu har da jami'ar yansanda mace mai dauke da juna biyu.

Wadanda aka kashe sun hada da DPO, jami'ar yansanda da wasu yansanda guda biyu kuma an shaida mace da aka kashe daga cikinsu mai suna CPL Joy Wellington.

Rahotanni sun ce ba farin hula ko daya da aka kashe a harin, duk da yake cewa akwai fararen hula guda uku da aka tsare su a bayan kanta.

Harin an gudanar da shi ne da misalin karfe 2:30 na dare ranar Litinin kuma rahotanni sun ce an dauki kusan awa daya ana gudanarwa

Kakakin hukumar yansanda na jihar Bayelsa Asinim Butswat ya ce yana jiran umaurni daga Kwamishinan yansanda na jihar kafin ya ce uffan a lokacin da manema labarai suka nemi jin ta bakinsa kan lamarin.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN