Yadda wata mata ta aika maigidanta barzahu bayan ta jibge shi da katako, karanta daliliLegit Hausa
A kullun abubuwan ban-al’ajabi da mamaki na ci gaba da faruwa a tsakanin mutanen wannan karni, har ta kai a yanzu zaman lafiya yayi karanci a tsakanin ma’aurata harma da wadanda suka yi auran soyayya.

A baya-bayan nan an samu lamura da dama wanda ke nuna inda mata ke sheka mazajensu lahira sakamakon sabani kowani rashin jituwa da ke gibtawa a tsakaninsu. Hakan ne ya faru a tsakanin wasu ma’aurata a yankin Darmnawa bayan gandun Sarki a birnin Kano, inda muka ji cewa wata uwargida ta yi ajalin maigidanta sakamakon rashin jituwa da ya gibta a tsakaninsu.

Wani mai amfani da shafin Facebook, Ahmad Deedat ne ya wallafa labarin, inda yace rikici ne ya fara kaurewa tsakanin matar da makwabtansu akan fadan yayansu, ana cikin haka ne sai mijin ya dawo ya tarar dasu.

Sai dai ba tare da bata lokaci ba mijin ya kora yaransa gida tare da matar tasa, sa’annan ya baiwa makwabtan hakuri. haka ta shirya masa mugunta. Sai dai hakan da maigidan yayi bai mata dadi ba saboda haka ta kulla masa wani tuggu. 


Yana shiga gida ta dauki wani katako ta rafka mashi ba kakkautawa har ya yanke jiki ya fadi matacce.
 

 
DAGA ISYAKU.COM

 Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN