Yadda wani dansanda ya yi mutuwar gaggawa a wajen gadi ana sati 2 ya Angonce


Legit Hausa

Iyalin wani jami'in dan sanda a kasar Ghana mai shekaru 42, kofral James Yaw Appiah, sun bayyana shakkunsu a kan yanayin mutuwarsa yayin da ya ke kan aiki. An samu gawar Appiah wanda aka fi kira da 'Antoa Cupers' a cikin rumfarsa ta aiki a kusa da asibitin gwamnati na Bawku inda aka tura shi ya yi aiki. 

A cewar iyalinsa, an gano cewa ya yi magana ta karshe a wayarsa ta hannu da Lady Prempeh, wata 'yar uwarsa mai rera wakokin yabo irin na addini, a ranar 4 ga watan Yuli da misalin karfe 2:30 na dare kafin daga bisani a samu gawarsa bayan wasu sa'o'i kalilan.

Wani babban wa a wurin marigayin, Dakta Nana Kusi Appiah Osraman, ya shaida wa wani gidan radiyon FM a Kumasi cewa rundunar 'yan sanda na son boye gaskiyar sanadin mutuwarsa ta hanyar kin sakin gawarsa ga danginsa.

Ya yi zargin cewa rundunar 'yan sanda ta boye gawar Appiah a dakin ajiye gawa don jikinsa ya rube a kasa ganin wata shaida da za ta nuna cewa kashe shi aka yi. Kazalika, ya zargi kwamandan 'yan sanda na yankin, DCOP Ampofo Duku, da hannu a cikin kisan Appiah, tare da bayyana cewa Marigayin ya taba fada masa cewa kwamandan na yi masa barazana a kan wata magana da ya ke da masaniya a kai, wacce kuma kwamandan ba ya son ta fita waje.

Dangin mamacin sun ce har yanzu an hana su ganin gawarsa, sati guda bayan mutuwarsa. Kafin mutuwarsa, marigayin, mai 'ya'ya biyu, na shirin angonce wa a karo na biyu a cikin makonni biyu masu zuwa.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN