Wata Tela ta maka uwargidan shugaban hukumar DSS a Kotu bisa zargin cin zarafi

Wasu mata masu dinkin zamani a birnin Abuja sun maka uwargidan Darakta janar  na hukumar DSS Mrs Yusuf Bichi Magaji gaban wata Kotun tarayya bisa zargin azabtarwa da kuma tsaresu da hukumar ta yi kamar yadda jaridar Daily trust ta ruwaito.

Matan guda biyu Agnes Ikrishi Ejim da Hadiza Usman wadanda ke zaune a Asakoro sun shigar da karan ne bayan sun yi zargin cewa jami'an hukumar DSS sun shiga gidansu ranar Lahadi 5 ga watan Mayu 2019.

A takardar shigar da kara, ta hannun Lauyansu, Agnes da Hadiza sun ce lamarin ya samo asali ne bayan uwargidan Darakta janar na hukumar DSS ta kawo masu dinki na atamfofi 12 ranar 22 ga watan Fabrairu 2019, kuma ta ce zata zo ta karba idan ta dawo daga tafiya da za ta yi zuwa kasar waje domin duba lafiyarta.

Matan sun ce bayan ta dawo sai suka kai mata dinkinta ranar 10 ga watan Aprilu kuma ta duba su daya bayan daya ba tare da wani korafi ba. Amma bayan mako uku sai kuma ta kira su ta ce bata gan Dankwalai uku ba daga cikin atamfofin.

Hakazalika sun ci gaba da cewa bayan matar DGSS ta kirasu cewa dole fa su fito mata da wadannan dankwalai, jim kadan sai ta zo tare da wasu jami'an DSS sanye da abin rufe fuska suka afka wa masu  gadin gidan da duka da karfe 8:00 na safe ranar Lahadi 5 ga watan Mayu.

Sun ce jami'an sun jawo su daga gida kuma rabin tsiraicin jikinsu ya bayyana tare da shan duka da wulakantarwa daga bisani aka garkame Hadiza a ofishin rundunar DSS daga ranar 5 zuwa 7 ga watan Mayu ba tare da umurnin Kotu ba.
 
DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN