Legit Hausa
An nemi gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da kuma
dan takarar kujerar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP a zaben kasa da ya gabata,
Abba Kabir Yusuf, da su bayyana a gaban kotun daukaka kara da kansu ba tare da
turo wakilai ba. Shugabar kotun daukaka karar zaben gwamnan jihar Kano, Jastis
Halima Shamaki, ita ce ta bayar da wannan umurni a ranar Talata 17 ga watan
Yulin 2019.
Jastis Shamaki ta hani gwamnan Ganduje da kuma Abba Kabir a
kan turo wakilai yayin zaman sauraron karar dake tsakanin su ta kalubalantar
sakamakon zaben gwamnan jihar Kano da aka gudanar a watan Maris. Babbar
alkaliyar yayin zaman kotun biyu da aka gudanar a baya, ta yi watsi da wakilan
manyan 'yan siyasar biyu inda ta nemi gwamna Ganduje da kuma Abba Kabir da su
bayyana a gabanta da kansu.
Yayin zaman kotun na
baya-bayan nan da aka gudanar, shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi
Abbas, ya shaidawa kotun cewa ya halarci zaman ne a matsayin mai wakilci ga
gwamnan Abdullahi Ganduje. Kazalika, wani hadimin tsohon gwamnan jihar Kano
Rabi'u Musa Kwankwaso, Yunusa Dangwani, ya bayar da shaidar kasancewar sa a
kotun a matsayin mai wakilci ga dan takarar gwamnan Kano na jam'iyyar PDP, Abba
Kabiru Yusuf.
Jastis Shamaki ta jaddada cewa, gwamna Ganduje da Abba Yusuf
su kasance cikin sani na cewar kotu ba ta ba su damar gabatar da masu wakiltar
su ba illa iyaka da su bayyana a gaban ta da kansu a duk sa'ilin da suka
bukata.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi