Wargi ya baci: Atiku Abubakar ya kwance ma wani Sanata zane a kasuwa, karanta dalili


Legit Hausa

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya kwance ma Sanata Elisha Ishaku Abbo Cliff zani a kasuwa.

Legit.ng ta ruwaito an dauki hoton bidiyon Sanata Abbo Cliff yana sharara ma wata mata mai shayarwa mari a wani shago dake babban birnin tarayya Abuja, wanda hakan ya harzuka yan Najeriya, kuma ya janyo cece kuce a shafukan sadarwa.

Atiku ya bayyana bacin ransa game da wannan lamari a shafinsa na kafar sadarwar zamani na Facebook, inda yace ya san Sanata Elisha farin sani, kuma bai ji dadin ganin bidiyon ba, amma ya bayyana cewa dolene a bari doka ta yi halinta. “Na kallo bidiyon dukan da Sanata Elisha Abbo yayi ma wata mata, ban ji dadin bidiyon ba, kuma bai kamata a lamunci irin haka ba, na san Sanatan sosai, amma doka a bayyana take, kuma dole ne shuwagabanni su yi jagoranci abin koyi.


“Don haka ina bashi shawara daya nemi gafarar matar dana yan Najeriya, ya mika kansa ga hukumar Yansanda, tare da tabbatar da cewa ya nuna hali nagari, haka zalika ina kira ga jam’iyyarmu ta PDP dasu dauki matakin ladabtarwa akansa, kuma Yansanda su tabbata sun yi abinda ya kamata.” Inji shi.

 A wani labarin kuma bincike ya nuna cewa Sanata Ishaku Abbo Cliff yana dauke da cutar sida, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito. An gane haka ne yayin da Sanatan yake neman gurbi a kwalejin horas da jami’an sojan ruwa dake garin Onne na jahar Fatakwal a shekarar 2004, inda hukumar kwalejin ta gano yana dauke da cutar sida, watau AIDS.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN