Wani tsohon Minista ya fadi yankin da zai karbi mulki a 2023 bayan Buhari

Legit Hausa

Tsohon minista kuma tsohon shugaban kungiyar dattawan Arewa, Paul Unongo, ya yi hasashe tare da kyautata zato a kan Arewacin Najeriya wajen samar da shugaban kasa tare da ci gaba da rike akalar jagoranci a zaben 2023. Dattijon na kasa ya bayyara hakan ne yayin wata hira da manema labarai na jaridat The Sun. 

Ya ce Arewacin Najeriya ke da mafi kololuwar cancanta ta ci gaba da riko da akalar jagorancin kasar nan a 2023. Unongo ya ce babban zaben kasa na 2019 ya tsarkaka cikin gaskiya da kuma adalci fiye da yadda ta kasance a babban zabe na 1993 a yayin da mafi rinjayen kaso na al'ummar kasar nan suka kadawa shugaba Buhari kuri'u wajen tabbatar da nasarar sa. 

Cikin kalami na sa, Unongo ya ce "fiye da kaso 80 cikin 100 na talakawan kasar nan sun shimfida aminci da kuma dogara a kan shugaban kasa Buhari tamkar wani abun bauta da ba za su taba juya masa baya ba." A yayin da dimokuradiyya ke ci gaba da samun gindin zama a kasar nan, mulkin Najeriya zai ci gaba da kasancewa a Arewa a yayin zaben 2023 duba da mafi rinjayen kaso na adadin al'umma a yankin." 

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan jaridar Legit.ng ta ruwaito, tsohon dan takarar kujerar shugaban kasa na zaben 12 ga watan Yunin 1993 a karkashin inuwa ta jam'iyyar SDP, Dr Uma Eleazu, ya debe tsammani da cewar akwai yiwuwar za a shafe babin Najeriya daga doron kasa a 2023. Read more: https://hausa.legit.ng/1248781-zaben-2023-mulkin-najeriya-zai-ci-gaba-da-kasancewa-a-arewa---unongo.html
 

DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN