Ticker

6/recent/ticker-posts

Wani mutumi ya yiwa matarsa yankan rago a gaban 'ya'yansu saboda taqi yarda ya kwanta da ita

Legit Hausa

An cafke Wani mutumi da aka bayyana sunansa da Anton Nuryanto, dan shekara 37, a Tanjung Priok, dake arewacin Jakarta, a Indonesia, da laifin kai wa matarsa hari bayan taqi amincewa ya kwanta da ita.
A cewar hukumomin kasar, Anton yana kwance da matar tasa mai shekaru 34 da kuma karamin dansu, ranar Juma'a da misalin karfe 5 na Asuba, sai yake tambayar matar tasa cewa yana so ya kwanta da ita.
Matar taki amincewa da bukatar mijin nata, inda shi kuma Anton ya tashi ya dauko adda yayi mata yankan rago akan idon karamin dansun.
"Yaron yayi shiru ne kawai ya kasa yin komai," shugaban hukumar 'yan sanda na Tanjung Priok ya bayyana hakan a gurin wani taron manema labarai a yau.
Cikin ikon Allah matar ba ta mutu ba har makwabta suka kawo musu dauki, inda shi kuma Anton ya ranta ana kare.
Daga baya an cafko Anton a kusa da gidansu, yayin da ita kuma matar aka kai wani babban asibiti domin ceto rayuwarta.
"Yanzu haka dai ta dawo hayyacinta har tana iya magana," in ji jami'in dan sandan.
An tisa keyar Anton zuwa gidan yari na tsawon shekara goma.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi