LegitHausa
Gwamnan jahar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya dauki alwashin
gina ma mabiya addinin kiristanci wani katafaren coci a fadar gwamnatin jahar
dake garin Lokoja, inji rahoton jaridar Guardian. Majiyar Legit.ng ta ruwaito
ana sa ran Yahaya Bello zai daura tubalin gina cocin ne a ranar Litinin, 15 ga
watan Yuli a wani taro da zai samu halartar manyan kiristocin jahar da suka
hada da shugaban kungiyar CAN reshen jahar Kogi, Bishop Ibenu.
“Addini magana ne na Imani, idan ya kasance bama girmama
addinan junanmu hakan zai janyo mana koma baya, musamman duba da cewa rashin
girmama juna yana lalata dagantakarmu a matsayin mutane yan adam.” Inji Yahaya
Bello.
Yahaya Bello ya bayyana haka ne ta bakin kaakakinsa, Onogwu Mohammed,
inda yace ya yi mamaki yadda tsofaffin gwamnonin jahar Kogi suka gagara gina
coci a fadar gwamnatin jahar, duk kuwa da cewa akwai babban masallaci a fadar.
A baya an yi gwamnoni uku a jahar Kogi, kuma dukkaninsu Musulmai ne, da suka
hada da marigayi Abubakar Audu, Ibrahim Idris da kuma Idris Wada, kuma
dukkaninsu yan mazabar Kogi ta tsakiya ne.
A wani labarin kuma, an fara samun baraka tsakanin
shuwagabannin siyasar jahar Zamfara, inda tsohon gwamnan jahar, Sanata Ahmad
Yariman Bakura ya yi kaca kaca da gwamnan jahar, Gwamna Matawalle. Yarima ya
gargadi Matawalle da cewa kotu ce ta bashi mulkin Zamfara ba wai jama’a ba,
kuma ya sani cewa shi fara haskaka shi a lokacin daya nadashi kwamishina a
gwamnatinsa tsawon shekaru takwas daga 1999-2007.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi