Legit Hausa
Shugaba
majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya kafa kwamiti na musamman domin
bincike cikin bidiyon da ya yadu a kafofin ra'ayi da sada zumunta wanda ke nuna
sanata Elisha Ishaku, mai wakiltar Adamawa ta kudu yana dukan mace.
Wannan
magana ya biyo bayan karar da da Sanata Uba Sani mai wakiltar Kaduna da tsakiya
ta shigar a zauren majalisa da safiyar Laraba, 3 ga watan Yuli, 2019 inda ya
bayyana yadda abin ke jawo cece-kuce a fadin kasa da duniya gaba daya. Sanata
Uba Sani ya bukaci majalisar dattawan tarayya da dau matakin hukunta Sanata
Elisha Abbo, kan wannan abin kunyan da yayi wanda ka iya batawa majalisar suna.
Shugaban
majalisar dattawa a jawabinsa ya bayyana cewa wannan zargi ne tukunna amma sai
an gudanar da bincike kafin a tuhumesa. Yace: "Da safen nan na samu
kiraye-kiraye da dama daga cikin gida Najeriya da kasashen wajen kan abinda ya
faru.
Bisa ga
wadannan kiraye-kiraye da bacin ran da yan Najeriya suka nuna da kuma jawaban
abokan aikinsa, na nada kwamitin domin binciken zargin zaluncin da ake yiwa
Sanata Elisha Abbo."
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi