Legit Hausa
Hukumar Civil Defence a ranar Talata ta gurfanar Abdulrazaq
Garuba, dan shekara 45 da ke da zama a yankin Olore Abegunde dake Illori bisa
zargin yiwa yarinya yar shekara biyar fyade.
Yayin da yake magana da manema labarai a Illorin, kakakin
hukumar NSCDC, Mista Ayodele Bello ya bayyana cewa an kama mai laifin ne a
ranar 30 ga watan Yuni bisa laifin yiwa yar makwabta mai shekara biyar fyade.
A cewar hukumar NSCDC, mahaifiyar wacce aka yiwa fyaden ta
nemi doki bayan ganin fitowar diyarta daga dakin mai laifin da jini a
kafafuwanta. “Karamar yarinyar ta bayyana yadda mutumin ya ja tad a kawarta
zuwa dakinsa kafin kawar ta gudu daga dakin, inda aka barta ita kadai a hannun
wanda yayi mata fyaden,” inji ta.
Bello ya kara da cewa mai laifin ya sanya yatsarsa a farjin
yarinyan ne, wanda hakan yayi sanadiyyar zubar jini. Ya bayyana cewa binciken
da aka yi a asibitin kwararru na jihar Kwara, Sobi a Illorin ya nuna cewa anyi
lalata da yarinyar.
Kakakin hukuman ya kara da cewa kwamandan NSCDC, Mista Bello
Ale ya bukaci iyaye da masu kula da yara dasu tabbatar da cewa sun mayar da
hankali kwarai da gaske wajen kula da yara don guje ma aikin miyagun mutane
akan marasa galihu.
Haka zalika, mai laifin, Garuba ya musanta zargin, inda ya
bayyana cewa baya gida a ranar da aka ce al’amarin ya faru. Garuba har ila yau
ya bayyana cewa wannan ya kasance karo na biyu da ake zarginsa da yiwa yara
fyade, inda ya ce na farko an zarge shi da yiwa yar shekaru bakwai fyade kuma
ya share mako guda a hannun yan sanda kafin a sake shi.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi