Tsegumi: Buhari zai haramta wanzuwar Shi'a a Najeriya

Akwai alamun cewa shugaba Muhammadu Buhari zai haramta kungiyar Islamic Movement of Nigeria wanda aka fi sani da suna Shi'a.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa haramcin zai fito ne a wata dokar shugaban kasa Terrorism Prevention Act wanda aka fara amfani da shi a zamanin shugaba Goodluck Jonathan aka haramta kungiyar Book haram.
Ana kyautata zaton cewa za a fitar da sanarwar kafin ranar Laraba 24 ga watan Yuli. Wannan ya biyo Bayan Wata ganawa ne da Buhari ya yi da manyan jami'an tsaro a fadar shugaban kasa bayan arangama da aka yi tsakanin yan Shi'a da yansanda da ya kai ga salwantar rayuka daga bangarorin guda biyu.

DAGA ISYAKU.COM
Previous Post Next Post