Tirkashi: Daga amsa kiran waya kawai sai ya tsinci kanshi a gidan masu garkuwa da mutaneLegit Hausa

Rundunar 'yan sandan jihar Legas ta kama Uba da Da da laifin yin garkuwa da wani mutumi mai suna Mathew Isichei Chukwuebuka mai shekaru 19, wanda yake hannunsu na tsawon kwanaki tara. A jiya Laraba da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan na jihar Legas, DSP Bala Elkana, ya ce mutumin da lamarin ya shafa ya fada hannun barayin ne a Ibadan, bayan kawai ya daga kiran waya da wata number da bai sani ba.

"Ranar 4 ga watan Yuli da misalin karfe 12:16 na dare, jami'an bincike na musamman sun fara binciken wani aiki da helkwatar 'yan sanda ta Abuja ta aiko musu zuwa garin Ibadan dake jihar Oyo. "Jami'an sunyi binciken nasu cikin kwarewa ta hanyar amfani da na'urori, inda a karshe suka kama mutane biyu masu suna; Thoa Akorede da kuma Muhibudeen Akorede.

 "Sun kuma samu nasarar ceto rayuwar Mathew Isichei Chukwuebuka, wanda yake hannunsu na tsawon kwanaki tara babu abinci. "A bayanin da ya bayar Mathew ya bayyana cewa an kira wayar shine, yana dagawa kawai sai ya tsinci kanshi a Ibadan, da zuwan shi sai aka bashi wani abu daga cikin wata bakar tukunya yaci.

"Yana ci hankalinshi ya fita a jikinshi, suka umarceshi da ya basu wayarshi, suka sanya wayar kira ya daina shigowa, sai na layin da suke neman kudin fansa dashi kawai ne yake shiga. "Sun kuma kwace duka kudin da ke wajenshi, kuma suna bukatar kari. Sun dauke shi zuwa wajen ATM, inda suka cire naira dubu guma daga cikin asusun shi. "Sun bukaci a biya kudin fansa naira miliyan talatin kuma a tura kudin cikin asusun mutumin Mathew," in ji shi. Kakakin rundunar ya kara da cewa tuni an hada Mathew da 'yan uwanshi. 


DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN