Tap di jan: Uwargida ta yanke al'auran maigida domin ya ki ya yi jima'i da ita

Wata mata mai suna Biatrice Acen yar shekara 35 ta sa wuka ta yanke al'aurar maigidanta mai suna Mr Okot dan shakara 45 saboda ya ki saduwa da ita bayan ta bukaci ya kwanta da ita ya ki a gidansa da ke kasar Uganda.

Majiyarmu ta ce Biatrice ta dawo gida ranar 30 ga watan Yuni da kafe 10 na dare, kuma ta bukaci mai gidanta ya sadu da ita duk da yake Biiatrice ta yi tatil da barasa, amma sai  Okot ya ki. Domin ya dauki lokaci yana yi mata haka domin ya zama horo a gareta saboda yawan shan barasaa da take yi.

Amma washegari bayan Okot ya dawo daga farauta kuma ya gaji, sai ya ci abinci ya kwanta, ammafa ciwo ya sa ya tashi sai ya ga ashe Biatrice ta yanke masa al'aura kuma ta ruga da gudu.

An kai Okot wani Asibitin Apac inda yake jinya, yayin da ya riga ya shigar da kara a ofishin yansanda kan matarsa Biatrice wacce ko a bara rahotanni sun ce ta karya masa kashin kafada sakamakon wani tashin hankali da ya auku a tsakaninsu bayan ta bugu da barasa.


DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN