Ta kwabe: APC ta kori mataimakin Oshiomhole na yankin arewa, ta bayyana dalil


Legit Hausa

Kwamitin gudanar wa (NWC) na jam'iyyar APC ya kori mataimakin shugaban jam'iyyar APC na yankin arew maso yamma, Inuwa Abdulkadir, bayan samunsa da laifin yi wa jam'iyya zagon kasa.

 A wani jawabi mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran jam'iyyar, Lanre Issa-Onilu, APC ta ce ta yanke shawarar korar Abdulkadir ne bayan bitar rahoton shawarar korarsa daga jam'iyyar da reshen jihar Sokoto da kuma mazabarsa ta 'Magajin Gari' suka yi a baya.

Jawabin ya ce: "Abdulkadir ya gaza yin amfani da damar da aka bashi domin ya gurfana a gaban kwamitin da NWC ta kafa ya tuhume shi domin ya amsa tambayoyi a kan zargin da wasu mambobin APC a jihar Sokoto ke yi masa.

"Biyo bayan dakatar da Abdulkadir da NWC ya yi, za mu mika shawarar korarsa, kamar yadda reshen jam'iyya a Sokoto ya nema, ga kwamitin zartar wa na uwar jam'iyya (NEC) domin dauka mataki na gaba."
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN