Shugaba Buhari ya koka kan hare-haren da aka kai mahaifarsa, ya yi umurnin daukar matakin gaggawa

Legit Hausa
Biyo bayan wani dan karamin al’amari da ya haddasa rikici da kashe-kashen rayuka a jihar Katsina a ranar Laraba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi umurnin daukar mataki na tsaro cikin gaggawa a jihar, da kuma hukunta wadanda ke da hannu a rikicin.
Shugaba Buhari ya gargadi makiyaya da al’umman garuruwa da su daina daukar doka a hannunsu ta hanyar tayar da rikici akan kowani abu, inda ya kara da cewa ya zama dole makiyaya da ke dawowa daga Kudu saboda lokaci na damuna su mutunta iyakokin manoma da jama’a, yayinda yace ya zama dole jama’a su janye daga kai ma makiyaya hari.
Shugaban kasar yayi ta’aziyya ga iyalan da suka rasa masoyansu a harin makiyayan, inda ya basu tabbacin cewa za a tsaurara matakan tsaro domin guje ma rikici mara ma’ana a tsakanin makiyaya da jama’an gari.
Shugaban kasar wanda ya jinjina wa gwamnatin jihar kan samar da kayyakin tallafi domin jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu na kare bayin Allah, yace gwamnatin tarayya za ta ci gaba da samar da yanayi ga jama’a ta yadda za su dunga gudar da harkokinsu ba tare da tsoron tozarci ko rikici ba.
Shugaban kasar ya umuri hukumomin tsaro a jiyar da sauran yankunan kasar baki daya das u yi aiki domin hana rikici, sannan su tabbatar da aminci a tsaninsu da jama’a da shugabannin yankuna.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN