Sarki Sanusi ya aika ma Ganduje da kudiri mai shafi 218

Legit Hausa
Masarautar Kano, karkashin jagoranci Sarki Muhammadu Sanusi II ta shirya wani kudiri da zai duba lamarin zamantakewar iyali don magance matsalolin auren wuri, sakin aure da kuma almajiranci a jihar.
Wannan kudirin dai har an mika shi zuwa ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje don ya aika zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano don tabbatar da shi ya zama doka.
Shugaban kwamitin masarautar Kano akan harkokin lafiya, Dr. Bashir Muhammad ne ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar a jihar Kaduna
Ya bayyana cewa ya dauki masarautar da wasu masu ruwa da tsaki tsawon shekara biyu don tsara wannan kudiri mai shafi 218. Ya kuma bayyana cewa idan aka tabbatar da kudirin ya zama doka, to zai taimaka wajen magance matsalolin zamantakewa musamman auren ‘ya’ya mata da kuma almajiranci.
Ya bayyana cewa “Eh akwai kudirin da mai martaba sarki Kano Sanusi ya shirya akan zamantakewar iyali kuma har ya mika shi zuwa ga gwamna don a isar da shi majalisa.”
“Dokar ta kare duk wani hakkin aure a musulunci bisa shari’ah, misali, an sanya ka’idojin da mutum zai cika kafin a bashi aure, dan gane da mata kuma, izuwa shekara nawa ne za a iya bada su aure” A cewarshi.
Ya kuma yabawa gwamnatin tarayya akan hubbasa da ta yi na magance matsalar almajiranci a arewacin Najeriya.
Da yake maida jawabi, wani mai rike da sarautar gargajiya daga jihar Kano, Yahaya Inuwa Abbas ya bukaci iyaye da su rinka saka ‘ya’yansu mata a makarantun koyan aikin asibiti don su zama ma’aikatan asibiti.
Ya bayyana cewa yana da kyau ‘ya mace ta samu wannan ilimin domin ta zama malamar asibiti ko kuma unguwar zoma. Ya bayyana cewa wannan ilimin na mata yana da matukar mahimmanci ga al’umma.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN