Na kashe kaina ne don guje wa damun mahaifiyata - Matashi mai shekaru 27


Legit Hausa

Wani matashi, Nsisong Okon Etim, mai shekaru 27, ya kashe kansa a garin Efiat Ikot Edo a karamar hukumar Uyo da ke jihar Akwa Ibom bayan ya yi zargin cewa mahaifiyarsa da dan uwansa da mutumin da yake haya a gidansa na yawan damunsa.

Marigayin, wanda ya kammala karatunsa na jami'a' ya bayyana hakan ne a cikin wata takarda da ya rubuta kafin mutuwarsa. "Na katse rayuwata ne saboda bakin ciki, domin na samar wa kai na sauki daga damu da damuwar da mahaifyata, dan uwana da mutumin da nake hayar sana'ar siyar da makamashin 'gas' a shagonsa ke saka ni koda yaushe, kamar yadda Nsisong ya rubuta.

Batun mutuwar matashin na cigaba da girgiza mazauna titin Ukpong Edet inda marigayin da mahaifiyarsa ke zaune. Wata majiya daga dangin marigayin ta bayyana cewa matashin ya kammala hidimar kasa tun shekarar da ta gabata kuma ya fara sana'ar sayar da makamashin iskar 'gas' bayan ya gaza samun aikin gwamnati.

Yar uwar marigayi Nsisong ta bayyana cewa marigayin ya kasance mai zurfin ciki da ba ya son tattauna matsalolinsa da kowa. Nsison ya kashe kansa ne ranar Talata, 23 ga watan Yuli, ta hanyar rataye kansa a jikin wata igiya da ya daura a rufin dakinsa bayan ya tube daga shi sai dan kamfai. Sai dai mahaifiyarsa, wacce ke cikin matukar halin dimuwa, ta kasa cewa komai ga manema labarai yayin da take ta zubar da hawaye a lokacin da aka binne Nsisong.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

 Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post