Matasan kasar Zuru sun gabatar da wata muhimmiyar bukata ga Gwamna Bagudu

Tsohon shugaban karamar hukumar mulki ta Zuru a kudancin jihar Kebbi Alhaji Muhammad Kabir Abubakar ya gamu da kauna tare da bege daga matasan kasar Zuru sakamakon abin da matasan suka kira ayyuka da ya yi tare da mutunci, amana, gaskiya da adalci wajen tafiyar da lamurran jagorancin karamar hukumar a cikin shekaru biyu da ya yi a matsayin Kantoman karamar hukumar. Sakamakon haka Kabir ya sami tagomashi tare da sambarka daga jama'ar kasar Zuru.

Hakazalika matasan sun yi wani kira na musamman ga Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu bisa wata bukata ta musamman dangane da shugabancin karamar hukumar mulki ta Zuru a wannan yanayi da aka fuskanta na sake samar da shugabanci a kananan hukumomin jihar Kebbi.

Latsa kasa ka saurari sauti:
DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post