Legit Hausa
Masu garkuwa da mutane sun sako magajin garin Daura, kuma
surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Musa Umar Uba da suka yi garkuwa
dashi tun kimanin watanni 2 da suka gabata.
Legit.ng ta ruwaito rahotanni daga garin Daura sun tabbatar
da haka, inda suka bayyana cewa a ranar Talata, 2 ga watan Yuli ne miyagun suka
sako Magajin Gari ya dawo gida. Idan za’a tuna a ranar 1 ga watan Mayu ne wasu
gungun yan bindiga guda hudu suka kai farmaki gidan Magajin garim Daura, inda
suka yi awon gaba dashi yayin da yake zaune a kofar gidansa bayan sallar
Magariba.
Shi dai magajin gari ya kasance kani ne ga mai martaba
Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, kuma tsohon kwanturola ne a hukumar hana fasa
kauri ta kasa watau kwastam, haka zalika yana auren Hajiya Bilki, diyar babbar
yayar shugaba Buhari, Hajiya Rakiya. Bugu da kari, babban dogarin shugaban kasa
Buhari, Kanal Muhammad Abubakar yana auren diyarsa Fatima.
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi