Kotun koli ta sanar da ranar da zata zauna kan shari'ar Atiku da Buhari


Legit Hausa

An dage sauraron karar da ‘dan takarar shugaban kasar Najeriya na zaben 2019 a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya kai gaban kotun koli inda ya ke kalubalantar shari’a da a ke yi a kotun zabe. A Ranar 30 ga Watan Yuli, 2019, babban kotun Najeriya ta dage zaman da ta ke yi domin sauraron korafin da Atiku Abubakar ya kawo na neman a yi watsi da hukuncin da Alkali Garba Muhammad ya yi.

Babban Lauyan ‘dan takarar na PDP, Paul Erokoro, ya nemi kotu ta karbi wasu karin hujjoji da bayani daga gare sa. Wannan ya jawo shari’ar ta tsaya cak inda sauran Lauyoyi su ka nemi a kara masu lokaci. A wani mataki da kotun ta fara dauka, za a dakatar da zaman wannan shari’a sai zuwa Ranar 20 ga Watan gobe na Agusta. Alkali mai shari’a Mary Peter-Odili da wasu Alkalai su dauki wannan hukunci.

A Ranar jiya Talata ne mai shari’a Mary Peter-Odili ta nemi a dakatar da sauraron wannan kara zuwa nan da mako uku. Kafin wannan lokaci wadanda a ke tuhuma za su kammala duk binciken da su ke yi. Babban Alkalin da ke sauraron korafin zaben shugaban kasa na 2019, Mai shari’a Garba Mohammed ya yi watsi da wani roko da Lauyoyin PDP su ke yi na bada dama su duba uwar-garken INEC.

Jam’iyyar PDP ta hakikance a kan cewa ita ce ta lashe zaben shugaban kasa kamar yadda kuri’un da hukumar zabe na INEC ta tattara a uwar-garken ta su ka nuna. INEC ta karyata wannan ikirari a gaban kotu. Yunus Usman shi ne Lauyan da ke kare hukumar zabe a kotu, yayin da shi kuma babban Lauya Wole Olanipekun, ya ke kare shugaban kasa. Lateef Fagbemi, shi ne Lauyan APC a wannan kara.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post