Karan kwana: Uwargida ta buge mijinta da ice, ya sheka lahira


Legit Hausa

Wata mata mai suna Bilkisu Isah ta jibgi mijinta, uban yayanta da wani makeken icce a gidansu dake unguwar Sabon Tahsa cikin garin Abaji na babban birnin tarayya Abuja, inda nan take ya fadi matacce. Jaridar Daily Trust ta ruwaito wani makwabcin ma’auratan mai suna Salihu ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis data gabata da misalin karfe 9:12 na dare sakamakon sa-in-sa data kaure tsakanin ma’auratan.

A cewar Salihu, Mijin matar mai suna Isah Egba ya rufe Bilkisu da fada ne akan fita da tayi daga gidansu ta bar yayansu 5 suna gararamba, kuma ba tare da neman izininsa ba, har sai karfe 8 na dare ta dawo, daga nan sai ya umarceta daga fitan masa daga gida.

Malam Isah bai tsaya nan ba sai ya rarumi uwargida Bilkisu da nufin fitar da ita da kansa daga gidan, hakan ne ya bata ma Bilkisu rai, inda ta rarumi wani katon icce ta maka masa a kai, nan take ya yanke jiki ya fadi, jini na ta kwarara daga kansa. Makwabtansu ne suka yi kokarin garzayawa dashi zuwa Asibitin Abaji cikin gaggawa, inda daga nan aka mikashi zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Abuja, amma bai yi tsawon rai ba, inda ya cika a cikin daren.

Da majiyar Legit.ng ta tuntubi rundunar Yansandan Abuja don jin ta bakinsu, sai kaakakinta, DSP Anjuguri Manzah ya tabbatar mata da aukuwar lamarin, kuma yace sun kaddamar da bincike akan lamarin, amma a yanzu suna farautar uwargida Bilkisu bayan ta ranta ana kare.
 
DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

 Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN