Legit Hausa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi nade-nade 11 a
ma'aikatu da hukumomi daban-daban tun bayan rantsar da shi a ranar 29 watan
Mayu, 2019. Jaridar Legit.ng ta tattara jerin sunayen mutanen da shugaba Buhari
ya bawa mukami ya zuwa yanzu, da kuma ma'aikatu ko hukumomin da aka nada su.
1. Saleh Dunoma – shugaban hukumar kula da filayen tashi da
saukar jiragen sama na kasa (FAAN)
2. Dakta Gambo Gumel Aliyu – Babban darektan hukumar dakile
yaduwar cutar kanjamau (NACA)
3. Farfesa Mohammed Nasir Sambo – Babban sakataren hukumar
inshorar lafiya ta kasa (NHIS)
4. Ahmed Idris – Babban akawun gwamnatin tarayya (AGF) a
karo na biyu.
5. Mele Kolo Kyari – Shugaban kamfanin dillancin man fetur
na kasa (NNPC) 6. Farouk Garba Said (daga yankin arewa maso yamma) – Babban
jami'i ai kula da harkokin kasuwanci a NNPC
7. Mr. Roland Onoriode Ewubare (daga yankin kudu maso kudu)
– Babban jami'i mai kula da harkokin hakar danyen mai a NNPC
8. Mustapha Yinusa Yakubu (daga yankin arewa ta tsakiya) –
Babban jami'in NNPC mai kula da tace man fetur da albarkatun cikinsa
9.Yusuf Usman (daga yankin arewa maso gabas) – Babban
jami'in NNPC mai kula da makamashin iskar Gas da lantarki.
10. Lawrencia Nwadiabuwa Ndupu (daga yankin kudu maso gabas)
- Babbar jami'ar NNPC mai kula da kasuwanci
11. Umar Isa Ajiya (arewa maso yamma) – Jami'i mai kula da
harkokin kudi Har yanzu ana jiran jin sunayen mutanen da Buhari zai bawa
mukamin ministoci a zangonsa na biyu.
A cikin makon nan ne kafafen yada labarai suka bayyana cewa
shugaba Buhari ya aika da sunayen mutanen da ya ke son bawa mukamin minista
zuwa ofishin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) domin a gudanar da bincike a
kansu, wanda da zarar sun kammala za a mika sunayen zuwa majalisa domin
tantance su da kuma tabbatar da su.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi