Jerin birane guda 11 da suka fi ko ina tsadar rayuwa a duniya

Legit Hausa
An bayyana biranen da suka fi ko ina tsadar rayuwa a duniya a wannan shekarar ta 2019. Birnin Paris, Singapore da birnin Hong Kong sunyi kunnen doki ne a matsayin biranen da suka fi ko ina tsadar rayuwa a duniya
Babban birnin kasar Faransa, wanda shine yake zuwa na daya a cikin jerin biranen tun daga shekarar 2003 zuwa wannan shekarar da muke ciki, inda a shekarar da ta gabata birnin Hong Kong da yake zuwa na hudu a cikin jerin biranen ya tsallako zuwa na uku.
Binciken da aka yi akan tsadar abubuwa sama da 150 a cikin birane 133 na duniya ya nuna cewa birane uku da suka fi ko ina tsadar rayuwa suna yankin Asia ne da kuma yankin Turai.
1. Paris: Birnin Paris yayi kunnen doki da birane guda biyu, babban birnin kasar Faransan yana zuwa a cikin jerin birane goma mafi tsada a duniya tun daga shekarar 2003 zuwa yanzu.
2. Singapore: Shine birnin da har yanzu bai sakko daga matsayin da yake ba tun a shekarar 2018, birnin Singapore yayi kunnen doki da birnin Paris da Hong Kong.
3. Hong Kong: Ya tsallake birane uku a cikin watanni 12 inda ya shigo cikin jerin birnin Paris da Singapore da suka yi kunnen doki.
4. Zurich, Switzerland: Babban birnin Switzerland shine ya zo a mataki na hudu a cikin jerin birane 133 da aka gabatar da bincike a kansu.
5. Geneva, Switzerland: Banda birnin Zurich, birnin Geneva yana daya daga cikin biranen da suke da tsakar kayan cikin gida, kayan kula da kai da kuma na shakatawa.
6. Osaka, Japan: Birnin Osaka ya zo mataki na shida a shekarar da ta gabata, kuma yanzu yayi kunnen doki da birnin Geneva na kasar Switzerland.
7. Seoul: Babban birnin Koriya ta Kudu yana daya daga cikin birane hudu a yankin Asiya da suke cikin jerin birane 10 masu tsadar rayuwa.
8. Copenhagen, Denmark: Wannan birnin na yankin Turai an yi binciken yana daya daga cikin biranen da suke da tsadar sufuri.
9. New York: Birnin New York yana daya daga cikin birane biyu na arewacin Amurka da suka shiga cikin jerin birane goman.
10. Tel Aviv: Birni na biyu da yafi kowanne mutane a kasar Isra'ila, wanda yake a mataki na 28 a shekaru biyar da suka gabata, yanzu shine ya dawo na goma a cikin jerin biranen, inda suka yi kunnen doki da birnin Los Angeles.
11. Los Angeles: Birnin Los Angeles da ake kira LA yanzu shine birni na goma da suka yi kunnen doki da birnin Tel Aviv a cikin birane mafi tsada a duniya.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post