Hotuna: Asiri ya tonu! An kama 'yar kabilar Igbo da ke yin jabun madaran Peak tana sayarwa jama'a


Legit Hausa

Hukumar kare masu amfani da kayayyaki ta kasa (CPC) ta bankado wata haramtacciyar masana'antar hada jabub madarar 'Peak' a kasuwar Eziukwu, Aba, a jihar Abiya. Jami'an hukumar sun yi nasarar damke wata mata da ke hada jabun madarar kuma ta bayar da muhimman bayanai a kan mutanen da ke taimaka mata wajen sayar da haramtacciyar hajar ta.

Tuni jami'an hukumar suka mika ta hannun jami'an 'yan sanda domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da ita. Wannan ba shine karo na farko da aka fara samun 'yan kasuwar Aba na kirkirar kayan amfani na jabu ba. Jami'an 'yan sanda da na hukumar kula da nagartar abin ci/sha da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta sha gano haramtattu masana'antun sarrafa ababen ci ko na sha ko kuma magunguna a kasuwar.

Masu kirkirar irin wadannan jabun kaya na jawo wa kamfanoni asarar kudade ta hanyar cushe kasuwa da jabun kayansu, marasa inganci. A wasu lokutan ma, su na amfani da sinadarai masu cutar wa wajen hada jabun kayayyaki.
DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN