Kwamishinan yansandan jihar Imo Mr Rabiu Ladodo, ya bayar da umurnin kama wani Safeton yansanda mai suna Okechukwu Nwanefi Bayan ya kashe wani matashi dan shekara 25 mai suna Ikenna Ukachi a Umuokeh, da ke karamar hukumar Obowo suka kone motocin yansanda da sauran kayaki.
Ranar Litinin da ta gabata ne Safeton ya bindige matashin a wani gidan sayar da abinci sakamakon wata gajeruwar muhawwara.
Daga bisani said ya gudu bayan ya tabbata cewa matashin ya mutu. Sakamakon haka matasa suka yi tawaye da ya kai ga zanga zanga zuwa caji ofis na yansanda da ke Obowo.
Majiyarmu ta ce Kwamishinan yansanda ya bukaci Safeton ya kawo kanshi ga yansanda ko kuma a kamoshi a duk inda yake.