EFCC ta kama wasu jami'an Gwamnatin jihar Sokoto guda 4 kan badakalar albashi

Hukumar yaki da yi ma tattalin arzikin kasa tu'annati EFCC a jihar Sokoto, ta kama wasu jami'an Gwamnatin jihar bisa zargin yin badakala da kudaden albashi har Naira dubu dari tara da tamanin N980.000.

Wadanda aka kama sun hada da Tukur yabo Daraktan ayyuka da gidaje na karamar hukumar Tureta; Hon. Abubakar Maigishiri,  Kansilan ayyuka da jindadi, Tureta LGA; Danjuma Ibrahim, Kashiya ma'aikatan jin dadi dawalwalan al'umma jihar Sokoto, da Sambo Abdullahi.

Kamasu ya biyo bayan takardar koke ne da aka shigar a kansu dangane da rashin biyan albashin Sokoto Marshal Corps/ Neighborhood Watch Operatives of Tureta Local Government sakamakon rashin biyansu albashin watannin Afrilu, Mayu da Yuni 2019.

Majiyar EFCC ta ce bincike ya nuna cewa Yabo ya hada baki da Maigishiri suka yi ruf da ciki kan albashin yan Neighbourhood 15, wanda ya yi sanadin rashin biyansu albashi wanda ya kai N300.000 duk da yake hukumar ta zakulo wasu daga cikin kudaden daga hannun su.


DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post