Dukan jami'in FRSC a bakin aiki a jihar Kebbi ya sa an garkame dan acaba a Kurkuku


Wata Kotun Majistare a garin Argungu na jihar Kebbi ta tasa keyar wasu matasa guda biyu, dan acaba Yahaya Yakubu da wani mai suna Yusha'u Mishanu zuwa Kurkuku bayan an gurfanar da su a gabanta bisa tuhumarsu da laifin dukan wani jami'in FRSC da ke bakin aiki a garin Argungu.

Mai magana da yawun hukumar FRSC a Sokoto Aliyu Maaji, ya ce wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne ranar 18 ga watan Yuli 2019, inda suka taru suka daki jami'in na FRSC da ke gudanar da aiki a garin Argungu.

An tuhume su da laifuka da suka hada da hana jami'i gudanar da aikinsa, kin bayar da kai a kamasu, cin zarafi da gangan ta hanyar zagi, duka da gangancin karya doka.

Alkalin Kotun Majistare Musa Alieru da ke garin Argungu, ya tasa keyar wadanda ake tuhuma zuwa Kurkuku har zuwa ranar 24 ga watan Yuni 2019 domin ci gaba da shari'a.

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post