Duba Jerin kudirori 17 da Buhari ya ki amincewa su zama doka

Legit Hausa
Shugaba Muhammadu Buhari ya ki amincewa da wasu kudirori 17, wadanda Majalisar Tarayya na 8 da ta shude ta aika masa domin ya sa musu hannu su zama doka.
Amma kuma ya sa wa wadansu kudirori guda tara hannu sun zama doka.
Babban Hadimin Shugaban Kasa a harkokin majalisar dattawa, Ita Enang ne ya bayyana haka a ranarLaraba, 3 ga watan Yuli a wajen wani taron manema labarai da ya shirya.
Sai dai kuma ya bayyana cewa shugaba Buhari ya yanke shawarar cewa ba zai aika wa sabuwar Majalisar Dattawa na 9 wasika a kan kudirorin da ya ki sa wa hannu ba, saboda ba za su yi wani abu a kan su ba.
Amma kuma Enag ya ce zai tuntubi dukkan majalisun biyu, ta Tarayya da ta Dattawa, domin yi musu bayanin dalilin rashin aminewar Shugaban kasa wajen ganin sun zama dokoki.
Ya ce babu wani abu da majalisar yanzu za ta iya yi domin tilasta wa shugaban kasa sa musu hannu, saboda doka ba ta ba su ikon yin hakan ba.
Daga cikin kudirori 9 da Buhari ya sa hannu suka zama doka, har da Dokar Gidauniyar ‘Yan Sanda, Hukumar FCT, Hukumar Inshora, Dokar Satar Fasaha da sauran su.
Akwai kuma dokar Hukumar Gudanarwar Hukumar Kiwon Lafiya a Matakin Farko ta FCT.
Daga cikin 17 wadanda Buhari ya ki amincewa su zama doka, akwai: Kudirin Jami’ar Adeyemi, Jami’ar Ilmi ta Jihar Kano, Jami’ar Alvan Ikoku, Jami’ar Ilmi ta Zari’a, Kudirin Dokar Kula da Dabbobi Marasa Lafiya, Kudirin dokar Hukumar Kula da Fina-finai ta Kasa da sauran su.
DAGA ISYAKU.COM Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN