Daga Abuja amaryata ta
gayyato wani kato suka kama daki a Otal - Mutumin da uwargidarsa ta caka
mai wuka ya yi tonon silili Read more: https://hausa.legit.ng/1248128-daga-abuja-amaryata-ta-gayyato-wani-kato-suka-kama-daki-a-otal---mutumin-da-uwargidarsa-ta-caka-mai-wuka-ya-yi-tonon-silili.html
Legit Hausa
Mutumin da uwargidarsa ta kusa hallakashi da wuka, Said
Hussein, ya fito duniya yana fallasa amaryarsa kan irin iya shegen da take
shekawa da ya kaiga dukanta har tayi nufin hallakashi. Sa'id Hussein bayan
samun lafiyarsa ya bayyana cewa sau talatin yana kama matarsa tana turawa wasu
mazaje ajnabiyya hotunan tsiraicinta a kafofin ra'ayi da sada zumunta. Idan ba
a manta ba dai, Fatima Hanan ta cakawa maigidanta wuka ne a ranar 22 ga Yunin
wannan shekara cikin tsakar dare da misalin karfe 1:30, a Unguwar Mai Kalwa,
Na’ibawa, karamar Hukumar Kumbotso, a Jihar Kano.
Kazalika, a cewarsa:
" Ina da cikakkiyar shaida ta yadda Matata ta gayyaci wani saurayi nata
daga Abuja, ya zo suka tare da ita a wani Otel da ke Unguwar Bompai, wanda dai
kawai ba na son kama suna." "Amma dai wannan abu ya faru ne, a 26 ga
watan Afrilun 2016, ba tare da la’akarin cewa ita matar aure ba ce.
Tana cikin wannan Otel daga misalin karfe 10:13 na safe har
zuwa 12: 16 na rana, ina nan da wadannan bayanai, don kuwa na’urar CCTV ta
wannan Otel ta nadi kafatanin wadanan bayanai da na ke fada a hali yanzu”, a
cewar tasa. Hussain ya ci gaba da cewa, a ranar wannan Juma’a dai da wannan abu
ya faru, na kama Hanan tana shan wasu kwayoyi a gidana tare da Shisha ta hada
shi da wani sinadarin kayan maye.
Sannan a ranar Azimin
karshe, ta zuba min guba a abincina, ta hanyar kada wa a cikin kwai kafin ta soya,
wannan ma ina da cikkakiyar shaida a kai." "A lokacin da abubuwa suka
yi tsamari ne, muka nemi Dakta Bashir, Limamin Masallacin Alfurkan, ya shiga
tsakani ya kuma ba mu shawarwari don gyaruwar al’amuran."
“A lokacin da muka je ganin Dakta Bashir tare da Matar tawa,
Mahaifiyar da yayanta dukkanin su a cikin motata na dauke su muka tafi tare.
"A gabansu ne kuma na zayyana wa Dakta Bashir irin miyagun halayenta
musamman a bangaren rashin kula da addini da kuma shaye-shaye ta kuma amsa ko
kadan ba ta musa ba." Amma Hanan, a wannan rana bayan mu dawo gida ne kuma
ta aika min wannan aika-aika da wuka bayan na kwace wayarta wadda take tura wa
samari da hotuna da kuma bidiyonta na batsa."
DAGA ISYAKU.COM
Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi