Da zafi-zafi: Yan Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a Masallacin Abuja


Legit Hausa

Mambobin kungiyar Musulmai yan Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a wani masallaci a Zone 3, Abuja, inda suka nemi saki shugabansu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa. Kungiya tau ma bayyana cewa wasu daga cikin mambobinsu da rundunar yan sanda Najeriya ta kama sun mutu aa tsare a rundunar tsaron.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar, Abullahi Musa, wanda ya zanta da manema labarai, ya bayyana da faro cewa za a fara zanga-zangar ne da zaran an kammala sallar Juma’a.

Kan mutuwar mambobinsu,Musa yace: bayanai abun dogaro da ke zuwa mana ya bayyana cewa yan sandan Najeriya sun tsare mambobin da ke zanga-zangar a saki Zakzaky ciki harda mata da kananan yara, tun ranar Ltinin, 2 a watan Yuli, tare da raunuka da ke barazana ga rayuwarsu sannan sukahana masu abinci da ganin likita.

“Zuwa yanzu,mutum uku sun mutu a hanun yan sanda saboda rashin kulawar ikita. Kamata yayi ace an kai masu zanga-zagar kotu cikin kasa da sa’oí 24,amma sun kwashe mako guda cur a hannun yan sanda." Idan za kutuna a ranar Litinin, 22 ga watan Yuli ne rikici ya kaure tsakanin yan sanda da Shi’a a lokacin wata zanga-zanga a sakatariya tarayya, Abuja wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
 

DAGA ISYAKU.COM

Shiga shafinmu na Facebook facebook.com/isyakunews

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/D9SKfH2BjM4Deldar0KkFN

Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi
Previous Post Next Post